Alfijr ta rawaito a zaman da aka gudanar a ranar juma a 13/1/2023 Alh Inuwa mijin Asiya
Balaraba Ganduje, ya bayyanawa Kotu cewa Balaraba ta bude masa gida tayi awon gaba da wasu muhimman takardun kadarorinsa da suke Abuja da Kano, tare da wasu manyan motoci guda uku!
Don haka yana bukatar a dawo masa da Kadarorin sa kafin ya amince da bukatar sakin na ta.
Inuwa ya bayyana haka ne ta bakin Lauyansa Inuwa ne ya bayyana hakan a madadin mijin a gaban kotun shari’ar musulunci dake filin
Hockey a Kano, karkashin jagorancin mai Shari’a Khadi Abdullahi Halliru, a cigaba da
zaman shari’ar da akeyi tsakaninsa da matarsa, ƴar gidan Gwamna Ganduje na Kano, wacce ta bukaci kotun ta raba aurensu, da ya shafe shekaru 16, da yaya tsanaki.
A nata bangaren Balaraba, ta bakin
lauyanta, Barista Ibrahim Nasarawa, ya musanta zargin awon gaba da Kadarorin mijn bayan amincewar biyan N50,000 a
matsayin sadakin mijin, amma lauyan Inuwa yace basu yarda ba, a basu lokaci domin bayyana adadin kudin da za’a biya su.
Sai dai a nasa bangaren mai shari’a ya bawa lauyan Inuwa mintuna 30 domin ya bayyana adadin kudin da suke bukata, wanda har lokacin ya cika bai samu damar bayyanawa ba, saboda haka aka dage zaman shari’ar har zuwa ranar 19 ga watan Janairu.
Daily NNigerian
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
To adai bi sannu ayi adalci. Tsakanin Mata da Miji sai Allah.
Allah ya bada ikon yin adalci tsakaninsu.