Yadda Nisabin Zakka Da Sadaki Da Diyyar Rai, Zai Kasance A Shekarar, 1445 Ah 2023/24

FB IMG 1696608891010

Yadda zata kasance a shekarar musulunci ta 1445 AH wajen fitar da hakkin Allah.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar Shari ah ta jihar Kano ta wallafa yadda nusabin zakka, sadaki da diyyar rai yake ta bana shekarar 1445 Ah 2023, kamar yadda ta saba duk shekara.

      MAFI KARANCIN SADAKI

₦50, 008. shine mafi karanci, amma mutum zai iya bada sama da haka bisa kyautatawarsa.

   Kimar Yanke Hannu A Sata

₦50,008 shi ne kimar da za a yanke hannu a idan mutum yayi sata.

NISABIN ZAKKA ZAI FARA DAGA ₦4000,695,00

Za a kasa wannan kucin gida (40) wanda zai zamanto ₦100,017 shi za a bayar

Idan kudin ya kai Miliyoyi, kowace Miliyan Ɗaya za a fitar mata da ₦25,000,00.

Kuɗin Azurfa, Nisabin zakkarsu zai kama, ₦341,946,5, abin da za a fitar shine ₦8,543,66.

Diyyar Rai A MUSULUNCI :
₦200,034,750,00.

Wannan kimar nisabin zai iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci,
sakamakon hawa da saukar Dinare da Azurfa.

NISABIN ZAKKAR DABBOBI
RAKUMA

RAKUMA: Daga (5 – 9) Akuya 1

Daga (10 – 14) Awaki 2.

Daga (15 – 19) Awaki 3

Daga (20 – 24) Awaki 4.

Daga (25) abin da yai sama za a fitar daga Rakuma.

SHANU: Daga (30) za a ba da Maraki

AWAKI/TUMAKI: Daga (40-120) za a ba da Akuya/Tunkiya.

Idan suka kai dari da ashirin da daya sai a ba da biyu har Zuwa dari biyu da daya, sai a ba da uku, daga nan kowace dari za a ba da ɗaya.

NISABIN ZAKKAR AMFANIN GONA

Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa goma (1/10) na noman ruwan sama, kwano (30).

Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa ashirin (1/20) na noman rani, kwano (15).

Wannan shine yadda zata kasance a wannan shekara ta 1445AH

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *