Yadda Masu Zanga-Zanga Suka Ragargaje Ƙofar Majalisar Dokokin Najeriya

Masu zanga-zangar cire tallafin mai da ƙungiyoyar ƙwadago ta kasa (NLC) ke jagoranta sun ɓalle ƙofar shigar majalisar dokokin Najeriya.

Alfijir Labarai ta rawaito rahotanni sun bayyana cewa fusatattun masu zanga-zangar ta NLC da takwararta TUC sun ɓalla ƙofar shiga majalisar ne bayan taƙaddama da jami’an tsaro da ke gadin harabar majalisar.

Masu zanga zangar sun isa wurin ne bisa jagorancin shugaban NLC Joe Ajaero da takwaransa na TUC Festus Osifo, inda suka buƙaci jami’an tsaron su buɗe musu domin su shiga su gabatar da korafinsu, amma jami’an tsaro suka ki.

Daily Trust ta rawaito cewa hakan ce tasa ’yan kungiyar suka yi kukan kura suka karya kofar suka kutsa cikin harabar majalisar.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *