An samar da wannan nusabin ne domin kula da hakkin Allah ga yan uwa musulmi.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumar Shari ah ta jihar Kano ta fitar da nusabin Dinare da Azurfa domin amfanar yan uwa musulmi.
YADDA AKE FITAR DA NISABI NA DINARE(GOLD)
A wannan lokacin Giram daya (1) na Gwal ana sayar da shi N47,067.00, don haka Giram 4.25 shi ne yake bayar da nauyin cikakken Dinare nasali dan Madina.
Dinare Ashirin (20) shi ne Nisabin Zakka wanda yake dauke da nauyin Giram 85 na ma’aunin zamani (sikeli).
A don hakaarashin Giram 4.25 na ma’aunin zamani shi ne a matsayin farashin Dinare daya (1).
Ta haka ne za a fitar da Nisabi a kowane lokaci, domin farashin Gwal yana hawa da sauka.
- Nisabin Zakka N4,000,695:00.
- Abin da za a fitar a bayar shi ne N100,017.4.
Mafi karancin sadaki N50,008.00.4.
Diyyar Rai N200,034,750:00.
YADDA AKE FITAR DA NISABI NA AZURFA (SILVER)
Nauyin Azurfa daya (1) yana daidai da 2.975 Giram na ma’aunin zamani.
Azurfa 200 shi ne nisabin Zakka na Azurfa.
Azurfa 200 zai ba ka nauyin Giram 595 na ma’aunin zamani, ko wanne Giram ana siyar da shi N574.7, saboda haka N574.7 x 595 zai ba ka N341,946.5, wannan shi ne Nisabin zakkar Azurfa wanda za a kasa kudin gida 40, zai kama N8,543.66 a ranar 5 ga Sept.2023.
Wannan Nisabi na Zinare da Azurfa ya dogara a kan farashin da suke da shi a kasuwar duniya,
Don haka yana iya canzawa sakamakon hawa da saukar su (Zinare da Azurfa), Allah ya sa mu dace.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo