Jami’an hukumar shiyyar Legas na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun cafke tsohon ministan kasuwanci da masana’antu, Charles Chukwuemeka Ugwuh, bisa zarginsa da hada baki da kuma zamba har N3.6bn.
Alfijir labarai ta rawaito an kama Ugwuh ne tare da Cif Geoffrey Ekenma a ranar 11 ga Janairu, 2024 a No.2, Musa Yar Adua way, New Owerri, Jihar Imo, bayan wata takardar koke ga hukumar daga wani bankin zamani kan zamba da ake zargin wani kamfani, Ebony Agro. Industries Ltd., mai alaƙa da tsohon Ministan.
Bincike ya nuna cewa Ugwuh da Ekenma, Manajan Darakta na Ebony Agro Industries Ltd., ana zargin sun samu lamuni daga bankin domin saye da samar da shinkafa.
Sai dai wanda ake zargin, a cewar mai shigar da kara, ya kasa cika hakkinsa na bankin, kuma duk kokarin da ya yi na ganin ya biya bashin kudin ya ci tura.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl