
Alfijr ta rawaito Sanatoci biyu na jam’iyyar PDP, Sanata Mathew Urhogide da Ayo Akinyelure sun fice daga jam’iyyar.
Sanarwar murabus din nasu na kunshe ne a cikin wasu wasiku daban-daban guda biyu da suka aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kuma aka karanta yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Sanata Urhogide ya wakilci mazabar Edo ta kudu a majalisar dattawa yayin da Sanata Akinyelure ke wakiltar Ondo ta tsakiya.

A cikin wasikar, Sanata Urhogide ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne saboda gazawar jam’iyyar PDP wajen daidaita rikicin mulki a jam’iyyar.
Ya ce, “Na ajiye mukamina na jam’iyyar PDP, nan take.
“Wannan shawara ta samo asali ne daga mummunan yanayin siyasa da ke tasowa a halin yanzu daga bambance-bambancen da ba a daidaita ba a cikin jam’iyyar PDP a matakin kasa musamman a jihara ta Edo.
“Wadannan rigingimu sun kai matakin da suka sa ba zai yiwu wani kamar ni wanda aka tabbatar da dimokradiyya ya yi aiki da girma kamar yadda na yi hasashe a tafiyar siyasa ta ba.
“Duk da haka ina godiya ga jam’iyyar da ta ba ni damar cimma burin bautar kasata a matsayin sanata mai wa’adi biyu – wanda kwarewa ta ba ni damar saduwa da aiki tare da dukkan abokan aikin ku.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ