Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama masu isar da sakonni guda uku saboda rarraba miyagun kwayoyi a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Lahadi a Abuja.
Babafemi ya ce jamiβan NDLEA sun gudanar da aikin binciken motoci da tsaiko a yankunan Gwarimpa, Jahi da Galadimawa a ranar Laraba, 30 ga Yuli. Sun kama wadanda ake zargi da suka hada da Sabo Sule (24), Samuel Nnamdi (28), da Idris Jibrin (28), inda aka gano gram 149.8 na Canadian Loud, wata irin tabar wiwi mai karfi a wajensu.
Babafemi ya kara da cewa an kama wasu da suka hada da Aliyu Abubakar (25) da Adekunle Agbabiaka (30) a kan hanyar Abaji-Gwagwalada dauke da kilogiram 91.1 na skunk, wata nau’in tabar wiwi, a ranar Asabar, 2 ga Agusta.
NAN.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan π
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ππ
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t