Gwamnatin jihar Sokoto ta ce a kundin tsarin mulkin Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmai bashi da ikon nada kowa a kowanne irin mukami.
Alfijir labarai ta ruwaito da yake jawabi a yayin taron jin ra’ayin al’umma kan dokar masarautu ta 2008, kwamishinan shari’a na jihar Sokoto, Barrister Nasiru Binji ya ce dokar masarautu da ake da ita a jihar ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce sashi na 76(2) na dokar ya ci karo da sashi na 5(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
“Sashi na 5(2) na kundin tsarin mulki ya bayyana karara, ikon nadawa na hannun Gwamna kai tsaye ko ra hanyar mataimakinsa ko jami’in Gwamnati da aka dorawa alhakin hakan.
“Don haka babu wani iko da aka baiwa Sarkin Musulmai na tin nadi”, inji kwamishinan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj