
Alfijr ta rawaito Jami’an tsaro sun harbe Ministan Kwadago, Kanar Charles Okello Engola, Karamin Ministan Kwadago, Aiki da Masana’antu a Uganda, a ranar Talata, daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa ya harbe shi a lokacin da yake shiga motarsa domin tafiya aiki.
Rundunar ‘yan sandan Uganda a yayin da take musayar bayanan farko game da kisan ministan, ta ce an kashe marigayin ne da misalin karfe 8:00 na safe a unguwar Kyanja da ke birnin Kampala.
Kakakin ‘yan sandan Uganda, Fred Enanga, ya ce, “Daya daga cikin masu gadin ministan ne ya yi harbin, wanda kuma ya yi harbi da dama a kusa da wajen.
Daga nan ne maharin ya gudu daga wurin zuwa cibiyar kasuwanci da ke titin Kyanja Ring Road inda ya shiga wani yanayi sai ya harbe kansa.”
Kakakin ‘yan sandan ya ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin.
Ya kara da cewa “Mun aike da kwararru a fagen aikata laifuka wadanda za su yi amfani da na’urorin zamani don tantance ainihin musabbabin kisan.”
A cewar jaridar The Independent, shaidun gani da ido sun ce sojan na sojojin Ugandan ya koka kan rashin biyansa albashi da kuma musguna masa kafin ya harbe kansa.
Hoton wurin aikata laifin da ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna gawar ministar sanye da shudiyar Kaunda a kwance cikin jini kusa da motarsa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇