Daga Aminu Bala Madobi
Tuni Gwamnan Dikko Radda ya aike da takardan tuhuma zuwa ga Mai Martaba Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman
Alfijir labarai ta ruwaito Gwamnatin Jihar Katsina ta tuhumi Majalisar Masarautar Katsina kan rashin halartar wasu Hakimai a wajen Hawan bikin salar idin babbar sallah na shekarar 2024.
A wata wasika mai dauke da sa hannun daraktan mulki na gidan gwamnati, Saki Rabiu Jibia ya sanyawa hannu, ya umurci majalisar masarautar da ta bayar da dalilan rashin halartar wasu hakimai yayin hawan.
Wasikar, mai kwanan wata 27 ga watan Yuni, 2024, ta yi nuni da cewa wata wasika da ta gabata daga Majalisar Masarautar mai kwanan wata 7 ga Yuni, 2024, kuma ta bukaci a bi kadin dalilan rashin halattar su cikin gaggawa.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan da hankula suka koma kan rikicin Masarautar Kano zuwa ga Sarkin Musulmi inda aka ce gwamnan sakkwaton ya gabatar da kudirin rage karfin Sarkin musulmi.
Rahotanni sun bayyana cewa izuwa yanzu ana cigaba da dakon jin ta bakin masarautar katsina kan dalilan da ya sa wasu hakimai suka ki halattar hawan babban sallah da ya gudana a masarautar.
Tuni Gwamnan Dikko Radda ya aike da takardan tuhuma zuwa ga Mai Martaba Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman
Bayanai sun ce Gwamnan yana neman Sarkin Katsina ya amsa tuhumar da yake masa akan wasu kudade da ya bashi domin ayi bikin hawan Sallah
Bincike ya nuna cewa Gwamnan ya bawa kowanne hakimi kudin hawan sallah daga asusun Gwamnatin jihar Katsina ta hannun Sarkin Katsina, kuma yace wajibine kowanne Hakimi mai albashi ya fito yayi hawan Sallah, ko ya sanya wakilinsa, to amma basu yi hawan ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj