Wata Sabuwa: Buhari Ya Tumbuke Shugaban Hukumar NYSC, Wata 6 Da Naɗa Shi

Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da cire Birgediya-Janar Muhammad Kakuh Fadah, wanda shine babban Darakta Janar na masu yi wa kasa hidima (NYSC) cikin gaggawa.

Hakan na zuwa ne kasa da watanni shida da hawansa mulki.

Ko da yake ba a bayyana dalilan korar Janar Fadah daga fadar shugaban kasa ba, wasu majiyoyi masu inganci a fadar ta Villa sun shaida wa PRNigeria cewa tsige shugaban NYSC din bai rasa nasaba da yadda Fadah ya nuna rashin iya aiki a fili. tsawon watanni 6 da ya yi yana duba harkokin NYSC ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *