Wata Sabuwa: An fara karanta hukuncin zaɓen gwamnan Kano ta manhajar ‘Zoom’

Alƙalai sun fara karanto hukuncin kotun sauraron ƙarfin zaɓen gwamnan Kano na 2023, sai dai ana karanto hukuncin ne ta manhajar zoom.

Ma’ana alƙalan kotun ba su samu halartar harabar kotun da kansu ba.

Sai dai lauyoyi da wakilan jam’iyyun da lamarin ya shafa suna zaune a cikin kotun inda suke kallo da sauraron hukuncin ta majigi.

Ya zuwa yanzu dai babu masaniya kan dalilan da suka sanya alƙalan suka gaza halartar zaman da kansu a harabar kotun da ke cikin birnin Kano.

Sai dai kafin ranar yanke hukuncin al’amuran siyasa sun yi zafi tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyu biyu, APC da NNPP, da ke hamayya da juna a jihar.

Kuma a baya babbar alƙaliyar kotun ta koka kan yadda wasu ke yunƙurin bai wa kotun cin hanci domin samun nasara.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *