Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda aka zargi Sarkin Daura na Jihar Katsina, Alhaji Dr. Umar Faruq Umar da taɓa wata mata mai yawon buɗe ido da ta kai masa ziyara a fadarsa, ta hanyar da ba ta dace ba.
Matar, wadda ke amfani da sunan ‘beduina’ a kafafen sada zumunta, kamar yadda ya bayyana a Vedio, ta yi wannan zargi ne a wani saƙon da ta wallafa bayan kammala rangadin kwanaki 30 da ta yi tana ziyartar sassa daban-daban na Najeriya.
A cewar bayaninta, lamarin ya faru ne ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, lokacin da ta kai ziyara garin Daura da ke Arewacin Najeriya.
Ta ce an kai ta wani katafaren ɗaki a cikin fadar, inda ta zauna tare da Sarkin suka tattauna.
Sai dai ta ce tattaunawar tasu ta sauya salo zuwa abin da ya sa ta shiga rashin jin daɗi, bayan da sarkin ya kama hannunta tare da fara wasa da shi.
A yayin bayyana abin da ya faru, matar ta ce ta shiga mamaki da firgici sakamakon abin da basaraken ya yi, inda ta sha gaya masa ya daina.
A cikin saƙon da ta wallafa, ta ce: “Na gaya masa, ‘Sarki a’a, a’a, a’a, bai kamata ka riƙa taɓa ni haka ba’, amma sai kawai ya ti ta dariya.”
Matar ta ce ba ta taɓa fuskantar cin zarafin lalata ba a iya yawon da ta yi a wadannan kwanaki 30 da ta yi a Najeriya sai da ta shiga fada irin Daura.
Ta ƙara da cewa, lokacin da suka miƙe tsaye, sarkin ya rungume ta, ya sumbace ta a kumatu, sannan daga bisani ya cafke ƙirjinta.
Ta ce abin da ya faru ya ba ta matuƙar ƙyama, kuma har yanzu tana ci gaba da tuna lamarin a zuciyarta.
Matar ta kuma bayyana zargin cewa tana tunanin ba ita ce mace ta farko da ta fuskanci irin wannan hali daga basaraken ba, sai dai wataƙila ita ce ta farko da ta samu damar ɗaukar bidiyon da ke nuna abin da ya faru.
Ta ce ta iya naɗan abin da ya faru ne ta gislashin da ta saka a fuskarta wadda ke ɗauke da kamara, kamar yadda HDT ta ciro hotuna daga bidiyon da ta naɗa.
Zuma Times
📢 KU BIBIYI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
WhatsApp: +234 0701 111 3809
KIRA: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
