Wata Kotu Ta Tsare Matashi Bisa Laifin Cin Amanar Kashe Mai Gidansa

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito mai shari’a A. Magaji na kotun Majistare ta jihar Kwara da ke zaune a Ilorin, babban birnin jihar ya bayar da umarnin tsare wani ma’aikacin gona da wasu makiyaya uku bisa zargin kashe wani manomi.

Alfijr Labarai

Wadanda ake tuhumar, Isiaka Sabi, Hassan Bature da Ardo Umaru, wadanda ake tuhuma da laifin kisan kai, ana zarginsu da kashe, Jamiu Ibrahim, mai shekaru 45, a duniya.

Rundunar ‘yan sandan ta yi zargin cewa wadanda ake tuhumar, a ranar 29 ga watan Yuni, 2022, sun hada baki tare da kashe Ibrahim na Idofin Odo-Ashe a karamar hukumar Oke-Ero ta jihar.

Rahoton na farko ya ce, “A wannan rana da misalin karfe 12 na safe wasu ‘yan bindiga biyar da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a unguwar gona ta Asalapa ta Idofin Odo-Ashe inda suka dauke dan uwansa Jamiu Ibrahim daga dakinsa zuwa wasu gonakin masarar Guinea da ke bayan gidansa, inda aka harbe shi da bindiga aka bar shi ya mutu a cikin  jini.

Alfijr Labarai

Rahoton ya kuma bayyana cewa wadanda ake zargin sun kashe Ibrahim ne saboda ya ki ba su kudi.

A wani bincike kwakwaf da aka gudanar a SCID, Ilorin, an gano cewa Sabi Isiaka, wanda ma’aikaci ne da ke yiwa mamacin aiki, ya gayyaci Hassan Bature da Umaru Ardo, mazauna kauyukan Fulani  kuma ya shirya yi wa Jamiu Ibrahim fashi a ranar 26 ga watan Yuli, amma ya kashe shi.

Shirin kai masa hari sun shirya shi a ranar 29 ga watan Yuni, 2022. “

A yayin bincike mai zurfi, Sabi Isiaka ya amsa laifin hada baki da Hassan Bature, Umaru Ardo, Janyo Dogo, domin yi wa marigayin fashi.

Alfijr Labarai

A zaman da aka yi ranar Alhamis, dan sanda mai shigar da kara, Thomas Adebayo, ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wadanda ake kara a gidan yari na tsawon kwanaki 21, har sai an kammala binciken ‘yan sanda kan laifin da ake zarginsu da shi.

Alkalin kotun, A. Magaji, ya tasa keyar wadanda ake kara a gidan yari na Oke-Kura.

Kotun kuma ta dage sauraron karar har zuwa ranar 1 ga Satumba, 2022, don ambata