Wata Kotu Ta Daure Wani Ɗan Sanda Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai

Alfijr ta rawaito wata babban kotun a Jihar Lagos ta yanke wa wani ɗan sanda Olalekan Ogunyemi, daurin rai dai rai saboda kashe wani mutum da je kallon kwallon kafa mai suna Kolade Johnson.

Alfijr Labarai

Ogunyemi, ɗan yan sandan wanda ke aiki tare da tawagar yaki da yan kungiyar asiri na yan sanda, ya harbe Johnson a ranar 31 ga watan Maris na 2019 a wurin kallon kwallo a Lagos.

Mai shari’a Adenike Coker ta samu wanda aka yi karar da laifin da aka tuhumarsa da shi ta kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai, inda ta ce dole ya yi a kalla shekaru 25 a gidan yarin.

Alkaliyar ta kuma yanke wtubabben dan sandan hukuncin daurin rai da rai bisa kisa amma ba na ganganci ba.

Alfijr Labarai

Olalekan wanda da farko aka gurfanar da shi kan gisar gilla, amma kotun ta same shi da kisa ba da niyya ba.

Yayin shari’ar, masu binciken sun kira shaidu bakwai yayin da wadanda aka yi karar suka kira shaidu biyu.

Yayin shari’ar, wani likita Dr Oluwaseun Williams, ya bada shaida cewa, an harbi Johnson, dan shekara 35 sai shida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *