Wasu ‘Yan Fashi Sun Kashe Mutane 3, Yayin Da Suka  Kai Hari A Banki da Ofishin ‘Yan Sanda

FB IMG 1718099197879

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari a hedikwatar ‘yan sanda reshen Abaji da ke Abuja tare da yin fashi a wani reshen bankin kasuwanci da ke yankin.

Alfijir labarai ta ruwaito maharan wadanda adadinsu ya kai kimanin 15, sun mamaye bankin da ofishin ‘yan sandan a lokaci guda a yammacin ranar Alhamis da misalin karfe 5:00 na yamma.

Ganau sun bayyana cewar an kashe dan sanda guda da biyu daga cikin wadanda ake zargin a yayin harin.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, wanda ta tabbatar da afkuwar wannan mummunan lamari ga manema Labarai a ranar Juma’a, ta ce jami’an rundunar a wani samame da suka yi da jami’an soji, sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka yi jagoranci ga wadanda suka jikkata.

A cewar PPRO, jami’an tsaro sun kama wasu mutane uku da ake zargin, ciki har da wani shugaban kungiyar masu laifin da aka bayyana sunansa Usman.

An tattaro cewa wasu fusatattun mutane a yankin sun kona gawar daya daga cikin wadanda ake zargin da suka mutu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *