Alfijr ta rawaito Rundunar yan sandan jahar Kano ta, tabbar da rasuwar wasu miji da mata a karamar hukumar Dawakin-Tofa dake jihar.
Al amarin ya faru ne a garin Kwa, bayan da ma’auratan Sulaiman Idris Mai shekaru 28 da matarsa Maimuna Halliru mai shekaru 20 aka daina jin duriyarsu, tun a ranar 2 ga watan Januaru 2023, shiru malam ya ci shirwa.

Shirun ne yasa Kakar Mijin ta garzaya dakin da suke ta bude kofar, shigarta ke da Wuya tayi arba da su kwance kan gado basa motsi da kuma hayaki yana tashi a cikin dakin.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar ƴan Sandan jahar Kano ya bayyana cewa, bayan samum rahotanne kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Mammam Dauda ya tura dakarun yan sanda karkashin jagorancin baturan yan sanda na Dawakin Tofa CSP Ahmad Hamza, tare da basu umarnin suje wajen cikin gaggawa.
SP Kiyawa ya kara da cewa bayan zuwan su ne, suka garzaya da matar da mijinta zuwa asibitin Murtala Muhammad dake birnin Kano Likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Binciken farko-farko ya tabbatar da cewa, an samu Kasko da Gawayi a ciki da sauran wuta da ta ke ci da alamun Hayaki yana tashi, sannan babu wata kofa da aka bari a bude.
Binciken ta bayyana zargin dalilin hayakin ne ya yi sanadiyar rasuwarsu da suka kasa numfashi har suka shiga yanayin wahala, don haka Jami an sun cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.
kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Mammam Dauda ya shawarci Al’umma, musammam ma a wannan lokaci da ake ciki na sanyi, lokaci ne da gobara takan tashi a cikin kankanin lokaci, don haka al umma su dinga kulawa da dukkanin wani abu na wutar lantarki ko wadda ake kunnawa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇