Wasu Mata Da Miji Sun Gurfana A Kotu Kan Zargin Sace Budurwa  Jihar Kano.

IMG 20180605 130113 099

An gurfanar da wasu ma’aurata kan zargin sace budurwa a Karamar Hukumar Tudun Wada da ke Jihar Kano.

Alfijir labarai ta rawaito mijin da matar sun gurfana a gaban Kotun Majistare da ke zama a unguwar Nomansland da ke Kano ne bisa zargin hada baki da kuma sace budurwar mai shekaru 17.

Rahotanni na nuni da cewar sun musanta zargin sace budurwar bayan dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Fago Lale, ya karanta musu tuhumar a gaban alkali.

Lauyansu ya nemi belinsu, yana mai cewa sun shigar da kara a babba kotun jihar suna neman a hana Kwamishinan ’yan sanda da kuma DPO na Tudun Wada tauye musu hakkinsu na dan Adam.

Amma alkalin kotun majistaren, Ibrahim Mansur Yola, ya bayyana cewa kararrakin ba su da alaka, saboda wancan na hakkin dan Adam ne, wanda ke gabansa kuma na zargin aikata laifi ne.

Sannan ya ce tsare wadana ake zargin a hannun hukuma ya fi zamansu a gidansu, saboda haka ya ba da umarnin tsare su.

Daga nan ya dage shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Janairun da muke ciki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *