Wasu Mahara Sun Ƙone Ofishin Hukumar Zabe INEC A jihar Ogun

Alfijr ta rawaito da safiyar ranar Alhamis ne gobara ta tashi a ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) dake karamar hukumar Abeokuta ta kudu a jihar Ogun, dake unguwar Iyana Mortuary.

Tashin gobarar dai ana zargin ‘yan bindiga ne suka kona ginin, inda suka zarce shingen, suka shiga cikin harabar, suka banka wa ginin wuta daga baya.

Ƴan bindigar wadanda ake tunanin sun kai su takwas, an ce sun zubawa biredi fetur sannan suka jefa cikin ginin da kuma wurare daban-daban don kone ginin.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce a dan dakace shi kuma ya yi alkawarin cewa zai sake kiran don jin kan lamarin.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida cewa jami’in tsaron da ke bakin aiki, Azeez Hamzat, ya yi wa ‘yan sandan waya da misalin karfe 1:00 na dare, cewa an banka wa ginin na hukumar zabe wuta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Vanguard

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *