Wani Ya Kashe Makwabcinsa Kan Wurin Ajiye Mota


Alfijr ta rawaito Wani mutum ya cakawa makwacinsa wuka ya kashe shi saboda sababin da suka samu a kan wurin ajiye mota.

Lamarin ya faru ne a yankin AJah na Jihar Legas, kamar yadda kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar.


Ya ce rundunarsu ta tsare wani mutum mai shekara 41 da ya caka wa makwabcinsa wuka a ciki, ya kashe shi nan take, bayan sun samu sabani kan wurin ajiye mota a kan layin Gbadamosi  da ke Rukunin Gidaje na Badore a daren Asabar.

Hundeyin ya ce an kai rahoton abin da ya faru ofishin ’yan sanda na Langbasa kafin wayewar garin Lahadi.

“’Yan sanda sun je sun dauki hoton abin da ya faru, kuma an kai gawar mutuwarin IDH da ke Yaba domin gudanar da bincike,” wanda ake zargin kuma ana tsare da shi.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *