Wani Miji Ya Ƙone Agololinsa (Yayan Matar) Su Biyar kurmus

Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta kama wani mutum mai shekaru 54 da haihuwa da laifin kona ‘ya’yan matarsa guda biyar a unguwar Fagun da ke garin Ondo.

Kakakin rundunar ƴan Sandan jahar Odunlami, Sufeto na ‘yan sanda, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, kuma ana kan binciken wanda ake zargin, yayin da kuma wadanda abin ya rutsa da su ke karbar magani a cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Owo.

Sai dai wani ganau da bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa matarsa ​​wadda ita ce mahaifiyar yaran da abin ya shafa ta bata masa rai saboda ‘yar rashin fahimtar juna lokacin da ya bukaci biyan bukatar sa yayin kwanciya.

Sai dai wata majiyar ta bayyana cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne saboda matarsa ​​ta hana shi hakkinsa na aure.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *