Wani Direban Jirgin Sama Yayi Karon Batta Da Maciji A Sararin Samaniya

Alfijr ta rawaito an yaba wa wani matuƙin jirgin ɗan Afirka ta Kudu kan nasarar saukar gaggawa da ya yi, bayan da ya lura da wani maciji nau’in gamsheƙa a ƙarƙashin kujerar zamansa.

Rudolph Erasmus ya ɗauko fasinjoji huɗu daga birnin Cape Town zuwa arewacin Nelspruit da safiyar ranar Litinin, amma saboda artabun da ya yi da gamsheƙar ya sa shi saukar gaggawa, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito

Direban ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Time Live cewa “ina duba ƙarƙashin kujerata, kawai sai na ga macijin na ƙoƙarin mayar da kansa ƙarƙashin kujerar”.

Sarar gamsheka zai iya kashe mutum cikin mintuna 30 idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

Minista harkokin sufurin jiragen sama ta Afirka ta kudu ya yaba da jarumtar Mr Eramus, kamar yadda shafin yanar gizo na news24 ya ruwaito.

Direban jirgin yace ya shiga yanayi mai rikitarwa wajen fada wa fasinjojin ainihin abin da ya sa ya yi saukar gaggawar.

Na fada musu cewa akwai matsala., akwai maciji a cikin jirgin. Ina da yaƙinin cewa yana ƙarƙashin kujera ta don haka za mu yi saukar gaggawa”.

Ya yi ƙoƙarin ganin ya yi saukar gaggawa a birnin Welkom dake Afirka da Kudu.

Injiniyoyin da suka caje jirgin ba su ga gamsheƙar ba, inji Mr Eramus.

Ya ce yana sa ran komawa bakin aikinsa a ranar Laraba.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *