Tsalle Daya! An Kama Wani Gardi Ya Shiga Ɗakin Kwanan Ɗalibai A Kano

Screenshot 20240316 111327 com.android.chrome edit 21609692942534

Jami’an Civil Defence a jihar Kano sun damƙe wani gardi mai suna Muhammad Munzali ɗan garin Ƙaura Gidan Damo a ƙaramar hukumar Shanono.

Alfijir labarai ta rawaito jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NSCDC, Ibrahim Abdullahi ne ya tabbatar da kamen a yau ranar.

Ya ce Jami’an sun damƙe wanda ake zargin ne da misalin karfe 10 na dare a ranar Laraba a lokacin da yake ƙoƙarin kutsawa cikin ɗakin kwanan ɗaliban na jami’ar Skyline wanda ke kan titin Sardauna Crescent, Nassarawa GRA,Kano

“Wanda ake zargin yayi ɓadda kama da shigar mata inda yayi ƙoƙarin kutsawa ɗakin kwanan ɗaliban, Ko Da aka cafke shi an same shi da layu a jikin sa,” cewar sa.

Ya kara da cewa, zuwa yanzu ana cigaba da gudanar da bincike domin gano hujjar sa na yin wannan kutse inda daga nan ne za a san wani mataki za a ɗauka.

Gardi
Gardi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *