Tsadar Rayuwa Ta Sanya Ana Zargin Wani Magidanci Ya Rataye Kansa

Wani magidanci mai suna Samaila Ilu mai shekaru 35 ya rataye kansa har lahira, sakamakon mawuyacin halin da yake ciki a jihar Jigawa.

Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin.

A cewarsa, “A ranar 17/08/2023 da misalin karfe 11:00 na safe ‘yan sanda sun samu rahoton cewa wani matashi mai suna Samaila Ilu mai shekaru 35 a kauyen Dungun Tantama a karamar hukumar Hausa ya bar gidansa.

Ya ce daga baya an tsinci gawarsa rataye akan bishiya da igiya, ana zaton ya kashe kansa ne.

Shiisu ya ce, tawagar ‘yan sanda sun kwashe gawar tare da kai shi asibiti domin a duba gawar.

Ya Ƙara da cewar tun daga lokacin aka mika shi ga ‘yan uwansa domin yi masa jana’iza.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *