Umarnin kotun ya kuma hana Ganduje shugabantar duk wata mu’amala da ta danganci jam’iyyar.
Babbar Kotun Jihar Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, daga jam’iyyar.
Alfijir Labarai ta ruwaito babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 4 da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako ta kuma haramta wa Ganduje bayyana kansa a matsayin dan Jam’iyyar APC.
Umarnin kotun ya kuma hana Ganduje shugabantar duk wata mu’amala da ta danganci jam’iyyar.
Mai Shari’a Naabba ya bayar da wannan umarni ne sakamakon neman hakan da Barista Dokta Ibrahim Sa’ad ya yi a madadin shugabannin APC na mazabar Ganduje da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa.
Kotun dai ta dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Afrilu, 2024.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk