Tirka-Tirka! Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan da fasinja ya gartsa wa ma’aikaciya cizo

FB IMG 1705511899853

Wani jirgin sama da ke kan hanyarsa ta zuwa Amurka, ANA, dole ya sauya akala ya koma Tokyo, bayan wani fasinja da ya bugu mai shekara 55 ya gartsa wa wata ma’aikaciyar jirgin cizo a hannu har ya yi mata ɗan rauni.

Alfijir labarai ta rawaito Mai magana da yawun kamfanin jirgin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP afkuwar lamarin.

A cewar kafar watsa labarai ta Japan, mutumin ya faɗa wa ƴansanda ya sha maganin bacci don haka ba zai iya tuna abin da ya faru ba.

Lamarin shi ne na baya-bayan nan cikin jerin matsalolin da fannin sufurin jiragen sama na ƙasar ya fuskanta a ƴan kwanakin nan.

Jirgin da ke ɗauke da fasinjoji 159 na saman tekun Pacific a lokacin da lamarin ya faru, abun da ya tilasta wa matuƙan jirgin juyawa suka koma filin jirgin Haneda da ke Tokyo.

Kamfanin jirgin ya ce a filin jirgin suka miƙa mutumin hannun ƴan sanda.

A ranar asabar jirgin saman ANA da ke zirga-zirga a cikin gida a ƙasar ta Japan ya juya inda ya fito bayan an gano ɗaya daga cikin tagogin jirgin ya tsage.

Mafi munin lamarin da ya faru da jiragen sama na Japan shi ne na ranar 2 ga watan Junairu, a filin jiragen sama na Haneda lokacin da jirgin ƙasar ya yi karo da ƙaramin jirgi na masu tsaron gaɓar teku.

Duka fasinjoji 379 da ke cikin jirgin sun kuɓuta, bayan ya kama da wuta, amma mutane biyar cikin shida da ke ƙaramin jirgin sun mutu.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *