Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin dan jaridar gidan talabijin na ARTV da harsashi ya same shi a gidan gwamnati a daren Juma’a.
Alfijir Labarai ta ruwaito wani dan jarida dake wakiltar gidan talabijin na Abubakar Rimi, a gidan gwamnatin Naziru Idris Ya’u, ya sami rauni sakamakon harbin bindiga a yammacin ranar Juma’a, a gidan gwamnati.
Sai dai takamaimai ba a san ta inda akai harbin ba, tuni aka garzaya da dan jaridar da ya jikkata zuwa asibitin gidan gwamnati.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, Mai Magana da yawun gwamnan jihar ya fitar a ranar Asabar, ya musanta faruwar lamarin inda ya bayyana shi a matsayin labari mara tushe.
Sanarwar ta kara da cewa, “An jawo hankalin gwamnatin jihar Kano kan wani rahoton daya fito daga kafafen yada labaran yanar gizo da ke nuna cewa wani harsashi ya sani wani dan jarida dake wakiltar gidan talabijin din ARTV a gidan gwamnatin jihar.
Labarin ya Sanya fargaba da kuma cece-kuce game da lafiyar ‘yan jarida da ke wakiltar ARTV a gidan gwamnati.
‘’magana ta gaskiya, Naziru Yau, wakilin gidan talabijin na jiha, babu wani harsashi da ya same shi”.
‘’Maimakon haka, ya samu raunuka daga tarkacen karfunan da ake fito da su daga wani gini da ake gyara a gidan gwamnatin jihar Kano.
Sai dai binciken da majiyarmy ta gudanar ya nuna cewa lamarin ya afku ne a masallacin da ke kusa da kofar shiga gidan gwamnati a daidai Inda aka kebe domin yin alwala, kamar yadda wanda abin ya shafa ya tabbatar.
Magana ta gaskiya, babu wani gini da ake yi a kusa da wajen sai dai aikin da ake yi a can bayan ofishin gwamna da ke kusa da African House a gidan gwamnati.
An sanar da SolaceBase tabbatacce cewa an kuma kai wakilin asibiti a safiyar yau don ci gaba da kula da shi.
Sai dai ana ci gaba da bincike kan dalilin yin harbin da kuma daga Ina aka harbo harsashin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk