Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na shirin nada Olanipekun Olukoyede a matsayin babban shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Alfijir Labarai ta rawaito Lauyan mai suna Olukoyede ya yi aiki a matsayin sakataren EFCC na tsawon shekaru biyu a karkashin tsohon shugaban riko Ibrahim Magu.
An dakatar da shi daga aiki tare da Magu a shekarar 2020 kuma ba a sake kiransa ba.
Kafin aikinsa na sakatare, Olukoyede shine shugaban ma’aikatan Magu.
Ana sa ran za a sanar da nadin nasa, wanda ke bukatar amincewar Majalisar Dattawa βnan ba da jimawa ba,β a cewar majiyoyin da ke da masaniya kan ci gaban.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai π
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo