Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su kwato bashin Anchor Borrowers daga waɗanda suka karba

N577bn daga cikin N1.103 793 587 359.70 har yanzu ba a dawo da su ba.

Alfijir Labarai ta rawaito a yayin da yake nuna damuwa da yawan kudaden da har yanzu wadanda suka ci gajiyar shirin Lamuni na Anchor Borrowers da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kafa, ba a dawo da su ba, Shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su bi wadanda ake bi basussuka da wadanda suka kasa biya.

Binciken Blueprint Weekend ya nuna cewa shugaban ya bayar da umarnin ne bayan bincike ya nuna cewa kimanin Naira biliyan 577 daga cikin Naira 1,103 793 587 359.70 da aka bayar har yanzu ba a dawo dasu daga wadanda suka karba ba, da suka hada da daidaikun mutane, kungiyoyin manoma da cibiyoyin kudi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wadanda suka kasa biya, wadanda tuni hukumomin tsaro suka tuntube su, kuma aka basu wa’adin ranar 18 ga watan Satumba su biya bashin duk da cewa wasu sun fara mayar da kudaden.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, bincike ya nuna cewa wasu kudaden da ba mu kwata-kwata ba a hannun masu zuba jari suke ba, sai dai a hannun bankunan da ya kamata su fitar da kudaden amma sun kasa fitar da dukkan kudaden da babban bankin ya ba su.

Da aka tuntubi Kakakin Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, Yace ba zai yi magana a kan binciken da ake yi ba, kamar yadda Kakakin Hukumar DSS, Dakta Peter Afunanya, ya ce bai dace da hukumomin tsaro da Shugaban kasa ya umurce su da su yi aiki da su ba.

A halin da ake ciki, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya (NPF), ACP Olumuyiwa Adejoibi, bai samu damar amsa kiran da akai masa ba don jin ta bakinsa,  a lokacin idan ya gabatar da wannan rahoton.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su kwato bashin Anchor Borrowers daga waɗanda suka karba”

  1. Ina daya daga cikin mabiya wannan jarida mai albarka, tabbas na ilmantu sosai,ina yiwa maaikatanta fatan alheri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *