Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin dakile barazanar tsaron kasa cikin kankanin lokaci, inda ya bukaci dakarun soji da sauran hukumomin tsaro da su jajirce.
Alfijir Labarai ta rawaito Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana haka ne a yayin bikin rufe bikin ranar sojojin Najeriya na shekarar 2023 (NADCEL) da kuma cika shekaru 160 na sojojin Najeriya da aka yi a ranar Alhamis a Ibadan.
Ya ce a shirye yake ya zafafa yaki da ta’addanci da kuma kare lafiyar ‘yan Najeriya a kowane lokaci.
“Ina tabbatar wa sojojin Najeriya da daukacin rundunar sojin kasar alkawarin da na yi na tabbatar da jin dadin su, kuma zan magance matsalar kayan aiki, rashin isassun kudade da sauran abubuwan da ke kawo musu cikas,” inji shi.
Tinubu ya kara da cewa gwamnatin sa ta samar da wata hanya da za ta magance dukkan kalubalen da sojojin ke fuskanta domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Masha Allah fatan alheri