Tinubu ya nada Indabawa da mutane 2 a matsayin kwamishinonin NUPRC

Tinubu Facebook

Shugaban ya kuma amince da sake sauya ofishin Dakta Kelechi Ofoegbu (Kudu maso Gabas), Babban Kwamishinan Ayyuka da Gudanarwa.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin kwamishinonin zartaswa guda uku a Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, har sai Majalisar Dattawa ta tabbatar da su.

Wadanda aka nada din sun hada da,

Bashir Indabawa, (Arewa maso Yamma), Babban Kwamishina, Bincike da Gudanar da Acreage;

Mr Enorense Amadasun (Kudu-Kudu); Babban Kwamishinan Ci Gaba da Samar da Kayayyaki

Mista Babajide Fasina (Kudu maso Yamma), Babban Kwamishina, Tattalin Arziki da Tsare-tsare.

Shugaban ya kuma amince da sake sauya ofishin Dakta Kelechi Ofoegbu (Kudu maso Gabas), Babban Kwamishinan Ayyuka da Gudanarwa.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Ngelale ya bayyana cewa matakin na da nufin kafa ka’idoji da al’adu wadanda ke kawar da gurbatattun dabi’u tare da karfafa himma da ayyukan kasuwanci na tushen ka’idoji a cikin masana’antar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *