Tinubu ya nada babban mai binciken kudi na tarayya (AUDITOR-JANAR)

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Mista Shaakaa Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya, kamar yadda Hukumar Kula da Ma’aikata ta Tarayya (FCSC) ta ba da shawarar, bisa ikon da sashe na 86 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara) ya ba shi,

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban kasar ya amince da nadin Mista Chira ne bayan da hukumar da’ar ma’aikata ta kasa (FCSC) ta gudanar da aikin tantance Mista Chira a matsayin wanda ya fi cancantar, wanda kuma ya samu nasara a jarabawar da aka yi a tsakanin dukkan wadanda suka cancanta a wannan ofishin.

Shugaba Bola Tinubu na sa ran sabon Odita Janar din ya tabbatar da amincewar da aka yi masa tare da cika kyakkyawan fata da ‘yan Najeriya ke yi game da aiwatar da ajandar sabunta ajandar gwamnatinsa.

Kamar yadda Chief Ajuri Ngelale
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman ya sanyawa hannu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *