Tinubu ya kori shugaban hukumar NIMC Tare Da Naɗa Madadinsa

Shugaba Bola Tinubu ya kori Darakta-Janar na Hukumar Kula da Shaidar ɗan Kasa, NIMC, Engr. Aliyu Abubakar Aziz.

Alfijir Labarai ta rawaito mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da bayanai, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

A cewar sanarwar, sallamar za ta fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Agustan 2023.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa shugaban kasar ya amince da nadin Engr. Bisoye Coker-Odusote don yin aiki a matsayin Muƙaddashin Darakta-Janar na hukumar.

Ya kuma amince da nadin Yusuf Buba Yakub a matsayin Darakta na Directorate of Technical Aid Corps, DTAC.

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *