Tinubu ya kara rokar kotun Amurka da kada ta saki wasu takardun karatunsa

Yan Najeriya za su kara tabbatar da cewa mai takardar da Shugaba Tinubu yake da’awar tasa ce, to ta mace ce.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaba Bola Tinubu, a ranar Litinin, ya roki wata mai shari’a a Amurka, Nancy Maldonado, da ta umurci Jami’ar Jihar Chicago da ta kare alfarmar bayanansa kamar bayanan shiga da rubuce-rubuce da jinsi da kuma sakin satifiket dinsa kawai ga kungiyar lauyoyin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku. Abubakar.

Lauyan shugaban kasa, Christopher Carmichael ne ya gabatar da wannan kudiri, wanda ya jaddada cewa, Tinubu ya rigaya ya tabbatar da mafi mahimmancin gaskiya ba tare da wata shakka ba.

Idan zaku tuna Alfijir Labarai ta bayyana muku cewa, Atiku Abubakar ya samu umarnin wani alkalin kasar Amurka, Jeffrey Gilbert, na CSU da ya umarci basa bayanan karatun Tinubu ga kungiyar lauyoyin sa.

Takardun da Atiku ya nema, ta hannun lauyansa, Angela Liu, sun hada da bayanan shigar Tinubu makaranta wato (Admission letter) da ranar da ya cike ya karba a CSU, da ranar kammala digiri,ln, da kyautuka da karramawar da tsohon gwamnan jihar Legas ya samu a jami’ar da dai sauransu.

Yayin da wa’adin da Gilbert ya bayar ya kara kusantowa a ranar Alhamis din da ta gabata, lauyoyin Tinubu sun tunkari Maldonado, suna masu cewa hukuncin da Gilbert ya yanke a baya yana bukatar wani alkali ya sake duba shi.

Bukatar sake duba da jinkirta odar har zuwa ranar litinin alkali na Amurka ya amince da shi.

Amma a ranar Litinin, kungiyar lauyoyin shugaban kasar ta roki Maldonado da ya saki takardar shaidar (certificate) kawai kuma ya hana sauran bayanan da Tinubu ke da shi.

Bukatar da lauyan ya gabatar a wani bangare, “Mafi mahimmancin gaskiya tuni Jami’ar Jihar Chicago ta riga ta bayyana a sarari, kuma babu sauran wata shakka:

Wannan batu ba shi da alaka da mai nema domin ba ya neman wani abu face bincike na adawa a kan abokin hamayyar siyasa.

“Alkalin majistare ya yi kuskure a fili wajen ba da damar cewa dole ne Jami’ar Jihar Chicago ta ba da amsa ga takardar da kuma gabatar da bayanan ga masu nema.

“Komai ƙanƙantar bayanai za a iya la’akari da su ‘don amfani’ a cikin shari’ar ƙasashen waje, don haka ya iyakance ga takardar shaidar da aka miƙa wa INEC ya isa.

Tsatstsefewa da tantance kutse cikin bayanai ba zai hana tabbatar da abinda ake so ba.

Wannan ci gaban na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani abokin takarar shugaban kasa, Olajide Adeniji, ya shaida a gaban kotun kasar Amurka cewa ya san shi kuma ya fafata da Tinubu a matsayin shugaban kungiyar Accounting Society Club a sashen kula da harkokin kasuwanci (Business Admin/Accounting) a cikin. Jami’ar Jihar Chicago.

A rantsuwar da ya yi a ranar 23 ga watan Satumba a kotun gundumar Illinois ta Arewa da ke Chicago, Adeniji ya yi rantsuwa cewa ya saba da Tinubu wanda shi ne shugaban Najeriya a yanzu.

Sai dai kungiyar Atiku ta lashi takobin kin amincewa da yunkurin da Tinubu ya yi a baya-bayan nan, inda suka ce a fili yake shugaban kasar na boye wani abu ga ‘yan Najeriya.

A wata zantawa ta musamman da wakilin Punch, Phrank Shaibu, mai ba Atiku shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan Atiku, ya ce suna da sa’o’i 48 kafin su mayar da martani kan bukatar da aka gabatar a gaban kotun Amurka.

Ya ce, “Muna sane da lauyan Tinubu ya shigar da kara a ranar Litinin yana rokon kotun Amurka da ta umurci Jami’ar Jihar Chicago ta saki takardar shaidar shugaban kasa kawai.

“Muna mamakin dalilin da yasa mutum zai bukaci su boye jinsinsa da sauran cikakkun bayanai a cikin rubutunsa na ilimi.

Amma mu (Tawagar lauyoyin Atiku) za mu amsa musu nan da sa’o’i 48 masu zuwa. Za a yanke hukuncin nan da Laraba ko Alhamis.”

Har ila yau, Daraktan Bincike da Dabarun kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa 2023, Pedro Obaseki, ya yi zargin cewa ikirarin da Tinubu ya yi na cewa sakin bayanansa ga jama’a zai haifar masa da bacin saboda mai takardar shaidar da ake takaddama a kai na mace ne ba na shi ba.

Da yake magana a wani taron Zoom wanda wani masanin ilimin halayyar dan adam mai zaune a Landan, Gold Emmanuel ya shirya a ranar Litinin,  Obaseki ya ce CSU za ta tabbatar da abin da jama ar Atiku ya rigaya ya sani ta hanyar bayyana tarihin Tinubu wanda ya kammala karatunsa a makarantar a ƙarshen 70s.

Ya ce, “’Yan Najeriya za su kara tabbatar da cewa mai takardar da Shugaba Tinubu yake da’awar tasa ce, to ta mace ce.

Mun riga mun san shi a matsayin gaskiya, amma muna neman sakin takardun a hukumance ta CSU. “

Da yake Karin haske Obaseki ya tambaya, “Abin da yake boye, mun riga mun sani.

Sakamakon zai karawa ‘yan Najeriya da dama kara bugun zuciya.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *