An kira taron ne domin jin ta bakin Gwamnonin Arewa ganin cewa wa’adin kwanaki bakwai na sojoji na mayar da shugaban da aka hambare ya cika.
Alfijir Labarai ta rawaito Shugaba Bola Tinubu a yammacin Lahadin da ta gabata ya gana da gwamnonin Arewa, wadanda jihohinsu ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ko da yake ba a bayyana makasudin taron ba, amma wata majiya daga fadar shugaban kasar ta ce taron na daga cikin shawarwarin da shugaban kasar ke yi kan halin da ake ciki a Nijar.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da
Ahmed Aliyu (Sokoto),
Umar Namadi (Jigawa),
Mai Malam Buni (Yobe)
Idris Nasir (Kebbi)
Dr Dikko Radda (Katsina).
Taron kamar yadda majiyar ta bayyana an kira taron ne domin jin ta bakin Gwamnonin Arewa ganin cewa wa’adin kwanaki bakwai na sojoji na mayar da shugaban da aka hambare ya cika.
Idan dai za a iya tunawa, kimanin mako guda da ya gabata ne shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka ba wa rundunar sojin da ta hambare zababben shugaban kasar Mohammed Bazoum daga mukaminsa.
Rundunar sojojin karkashin jagorancin Abdourahamane Tchiani, shugaban kungiyar CNSP ta kasa, ta karbi ragamar mulki bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum, a ranar 26 ga Yuli 2023.
Idan za a tuna shugabannin ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Tinubu a wani taro da aka yi a Abuja ya bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga rundunar sojin Jamhuriyar Nijar da ta mayar da Bazoum a matsayin zababben shugaban kasa ta hanyar dimokuradiyya ko kuma a fuskanci tsauraran takunkumi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI