Taraliya! Saurayin Mai Awara Ya Watsa Mata Tafasasshen Mai

Screenshot 20240805 142823 Chrome

Saurayin wata budurwa mai sana’ar awara ya yi mata wanka da tafasasshen mai da take suya da shi a yankin Samarun Zariya da ke Jihar Kaduna.

Alfiiir labarai ta ruwaito matashin ya yi wa buduwar tasa mai suna Hussaina wannen danyen aiki ne saboda ta nemi taka masa burki a wurin sana’arta, lokacin yake tsaka daukar awara da take soyawa yana cin.

Bayan saurayin ya yi ta daukar awara yana a dangwalala a yaji yana ci ne Hussaina ta yi masa magana cewa ya daina, lamarin da ya kai ga cacar baki a tsakanin masoyan.

Amma jama’a da ke wurin suka shiga tsakani aka raba su, shi kuma gogan ya yi tafiyarsa.

Ashe labewa ya yi, daga bisani kafin su ankara ya zo ya dauki kaskon suyan awarar ya sheka mata a jikinta.

A halin yanzu dai, iyayen Hisssana wadanda masu karamin karfi ne da suka dogara da sana’ar, suna rokon jama’a da kungiyoyin kare hakkin dan Adam su kawo musu dauki, domin yi mata magani da kuma kwato mata hakki.

Shaidu sun bayyana cewa saurayin da ake zargi ya yi wa budurwar wannan aika-aika ya yi kaurin suna wajen tayar da zaune tsaye.

Wani shaida ya bayyana cewa a kwanakin baya wanda ake zargi ya caka wa wani matsahi almakashi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar barin jikinsa.

Idon Gari

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *