Daga Baba Usman Gama
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa kungiyar Sahel Alliance da wasu kasashen Yammacin Afirka suka yi ba zai karkatar da hankalin ECOWAS daga ayyukan da take yi ba.
Sanatoci sun sallama albashinsu na Disamba ga mutanen Tudun Biri na jihar Kaduna.
Jirgin sojin Najeriya ya halaka gomman ‘yan ta’adda da baburansu 18 a cikin jirgin ruwa a jihar Neja.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce babu wata hujja da za ta sa Najeriya ta kasa shiga cikin kasashe mafi arziki a duniya.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta samu nasara halaka wasu ‘yan bingida a jihar Naija ciki har da wani gawurtaccen ɗan bindiga da ya jima yana addabar jama’a, mai suna Yellow Jambros.
Mutum 16 sun rasu 27 sun ji rauni a hatsarin mota a hanyar Kaduna-Abuja.
Gwamnan Katsina, Dikko Raddah, ya jagoranci fatattar ’yan bidiga a kauyen Zakka a Karamar Hukumar Safana ta jihar yare da ceto mutum 1.
Wani magidanci a jihar Bauchi ya yi yunƙurin halaka matarsa domin samun damar sayar da talabijin dinsu ya ƙara kuɗin jari a shagonsa.
Wasu masu gasar ’yar-kuren shan miyagun kwayoyi a bikin daurin aure a anguwar shola dake jihar Katsina sun fada hannun hukumar NDLEA.
Firaministan Falasɗiinawa Mohammad Shtayyeh ya nemi ƙasashen duniya su saka wa Isra’ila takunkumai saboda luguden wutar da take yi a kan Zirin Gaza.
Isra’ila ta ce an kashe mata sojoji 425 da raunata 1,593 tun daga 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu.
EPL: Everton ta sami nasara akan Chelsea da ci 2:0 a wasan yau.
EPL: Manchester City ta sami nasara akan Luton da ci 2:1 a wasan yau.
EPL: Fulham ta sami nasara akan West Ham da ci 5:0 a wasan yau.
Laliga: Atlentico Madrid ta sami nasara Almeria da ci 2:1 a wasan yau.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp