Daga Baba Usman Gama
‘Yan bindiga sun shiga Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ranar Litinin da daddare inda suka je kasuwar mini market suka kwashi kayan abinci da sauran abubuwa, in ji shugaban Jami’ar Farfesa Lawal Suleiman Bilbis. Sai dai jami’an tsaro sun fatattake su.
EFCC ta samu izinin cafko Diezani daga Turai ta fara shirye-shiryen taso Keyarta.
Kungiyoyin kwadago sun janye shirin yajin aiki a Najeriya.
Kimanin mutum 40 ne ake zullumin sun bace bayan wani hatsarin kwalekwale a Karamar Hukumar Yauri a Jihar Kebbi.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Rabi’u Usman Baba bisa rasuwar ’ya’yansu Sharif Fatuhu da Nafssuzzakiyyu a hadarin kwale-kwale.
Jami’ar jihar Chicago da ke kasar Amurka, ta damkawa Atiku Abubakar takardun karatun shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mutum 4 ‘yan gida 1 sun mutu sakamakon jan su da lantarki ya yi bayan tashin wata gobara a yankin Dinyavoh a birnin Jalingon Jihar Taraba.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Bosun Tijjani ya kaddamar da wani bankin zamani na yanar gizo mai suna ‘Kayi Bank’ wanda Alhaji Saadina Dantata ya kirkira ya samu sahalewar wasu kasashe na hannun jari kamar Saudiyya.
Tsohon shugaban Amurka Trump yace tuhumar da ake mishi a kotu wasan kwaikwayo ne.
Gwamnatin Iran ta yi afuwa ga fursunoni 1,000 albarkacin ranar Maulidi.
Amurka ta jaddada goyon bayanta ga Turkiyya kan yaki da kungiyar PKK.
An ayyana makokin kwana uku bayan ‘yan bindiga sun kashe sojojin Nijar 29.
EPL: Chelsea ta sami nasara akan Fulham da ci 2:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb
Good plan for the success