Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Talata 20/06/1445AH – 02/01/2024

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya amince da dakatar da Halima Shehu daga muƙaminta na shugabar hukumar jindaɗin al’umma ta ƙasa (NSIPA), bisa zargin tafka almundahanar kuɗi.

Gwamnati ta dauki matakin dakatar da amfani da takardun digiri da suka fito daga makarantun jamhuriyyar Benin da Togo.

Matatar garin Fatakwal ta fara gwajin tace danyen man fetur.

Ministan harkokin cikin gida yace rashin tausayi ne a ce sai mace ta je Abuja za a yi mata canjin suna a fasfo.

Hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ƙara wa’adin biyan kuɗin aikin Hajjin shekarar 2024

Hukumar Zaɓen Liberiya ta karrama Yakubu, Shugaban INEC da kambin gwarzon ƙara wa dimokraɗiyya karsashi.

Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Garam da ke jihar Neja inda suka yi garkuwa da mutum 3.

Gwamnan jihar Gombe ya ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci, a wani zagaye na shirin rage raɗaɗi ga talakawa da sauran masu rauni 90,000 da ke cikin al’umma.

Jirgin kamfanin Japan Airlines ya kama da wuta saidai an kuɓutar da fasinjoji kusan 400 da ke cikin jirgin.

Manyan janar din Sudan na musayar zafafan kalamai gabannin sulhu.

Red Crescent ta ce harin Isra’ila ya kashe mutum biyar a ofishinta.

Yawan mutanen da suka mutu a girgizar ƙasar Japan ya karu zuwa 48.

Somaliya ta bayyana yarjejeniyar Habasha da Somaliland a matsayin takalar faɗa.

Wani mahari ya caka wa jagoran ‘yan adawar Korea ta Kudu wuka a wuya.

Iran ta aike da jirgin yaki zuwa Tekun Maliya ba tare da bayyana dalili ba.

An cafke mutanen da ake tuhuma da kashe fitaccen dan tseren gudun Kenya.

Birmingham ta sallami Rooney daga matsayin koci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *