Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Talata 10/10/2023 – 25/03/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Wike ya bayyana wa jami’an tarayyar Turai cewa su taimaki tattalin arzikin Najeriya su daina shiga harkokin siyasar Najeriya

An kama motoci 69 a cikin shirin tsaftace Abuja

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani malamin addinin musulunci da dan uwansa a jihar Kogi

NECO 2023: Kashi 61% na dalibai suka sami sakamako mai kyau a darussa biyar da suka hada da Ingilishi da lissafi

Tsohon Minista ya ce cire sunan Shetty a cikin ministoci ya nuna cewa har yanzu akwai masu juya gwamnati

Anyi garkuwa da wasu daliban jami’ar jihar Nasarawa

Gwamnatin jihar Lagos ta rufe cocina da wuraren shakatawa kan hayaniya

Gas din girki ya kai N1,200 a kan Kg

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Aiyedatiwa ya janye karar da ya kai majalisar dokoki da Akeredolu

Sojojin Israela sun ce sun karbe iko a kan iyakan Gaza

Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Talata

Gwamnatin Najeriya ta musanta mayar da tallafin man fetur.

Ministan brinin tarayya Wike zai hada kai da Isra’ila don samar da tsaro a Abuja.

ISIS: An kama mutum 3 da makamai a Abuja.

Janar Yakubu Gowon ya musanta rahotannin da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa.

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon kayan abinci domin tallafawa al’umma don rage raɗaɗin talauci da kasar ke fama da shi.

Ƴan Shi’a sun yi tattakin goyon bayan Falasɗinawa a Abuja.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta dakatar da dan takarar gwamna na APC, Timipre Sylva, daga yin takara a zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban.

Algeria ta janye shiga tsakanin da ta ke a rikicin Nijar bayan juyin mulki.

Hamas ta yi barazanar kashe ilahirin mutanen da ta kama a Isra’ila.

Farashin man fetur ya tashi a Duniya sakamakon yakin Isra’ila da Hamas.

Angola ta dakatar da shirin janye tallafin man fetur saboda fargabar zanga-zanga.

Ana gudanar da zaben shugaban kasa a Liberia.

Kotun Kenya ta dakatar da batun tura dakarun ƙasar Haiti.

Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta tabbatar da yunkurin shiga tsakanin Hamas da jami’an Isra’ila.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

One Reply to “Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Talata 10/10/2023 – 25/03/1445AH”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *