Daga Baba Usman Gama
Majalisar dattijan Najeriya na son a tsagaita wuta a Gaza.
Ƙungiyar Mawaƙan Arewa ta kai wa tsohon shugaban Najeriya, Muhamadu Buhari ziyara a gidansa da ke Daura.
Kotu a Kano ta daure Garzali da ya kusa yi wa ‘yar shekara 13 fyade.
Ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC sun kira babban taron majalisar zartarwa wanda suka bayyana da na musamman a Abuja.
Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari a kauyen Sayaya da ke karamar hukumar Matazu a jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutum biyar.
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 40 domin aiwatar da wasu manyan ayyuka a fadin Jihar.
Kotu ta aika boka da wasu mutane 5 gidan yari saboda sun damfari tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Timothy Owoye, tsabar kudi har naira miliyan 38 da yada bidiyon tsaraicinsa.
Rundunar tsaro sun fara kai samame mabuyar yan daban siyasa a jihar Kogi.
Wasu tsageru da ake zargin ƴan daban siyasa ne sun kai hari gidan wani jigon jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa, Chief Diekivie Ikiogha.
A karo na farko, an gudanar da Taron Mata Musulmai na Duniya, wanda a wannan shekarar Saudiyya ta karɓi baƙuncinsa.
Barayi sun ritsa ministar sufuri ta Afirka ta Kudu da bindiga, sukayi mata fashi bayan abin hawanta ya tsaya a babban titi lokacin da take canza fasasshiyar taya.
Nijar ta nemi Togo ta shiga tsakani a rikicinsu da Ecowas.
Ƙarin ƴan ƙasashen waje masu fasfo za su bar Gaza a yau.
An kama ‘yan ta’addan da suka tsere daga gidan yari a Tunisia.
Japan ta ce ƙasashen G7 za su ci gaba da taimakawa Ukraine a yaƙinta da Rasha.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp