Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya ba da umarni a yi cikakken bincike kan kisan masu taron Mauludi kusan 90 da wani jirgin soja ya jefa wa bom a Jihar Kaduna.
Babban Hafsan Sojin Ƙasa Janar Taoreed ya halarci jana’izar mutanen da harin soji ya kashe bisa kuskure ranar Lahadi a jihar Kaduna.
Ƙungiyar Dattawan Arewa ta yi Allah-wadai da luguden bam kan fararen hula a Kaduna.
Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin jingine hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Sokoto ta yi na kwace motoci 50 na alfarma.
Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya yi alkawarin Gwamantin Tarayya za ta biya diyyar mutanen da harin bom din taron Mauludin Kaduna ya rutsa da su.
Dahiru Bauchi ya nemi Tinubu ya biya jinin Musulmin da jirgin soji ya kashe a Kaduna.
Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga sojan da ya kashe fitaccen malamin Musulunci a Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.
Akalla mutum 85 ne suka mutu a harin jirgin sama da sojojin Najeriya suka kai a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Iyayen daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara da aka sace sun gudanar da zanga-zangar lumana a gidan gwamnatin jihar.
Sojojin Nigeria sun taba kashe makiyaya a jihar Nasarawa tunda aka ce za’ayi bincike Haryanzu babu Sakamakon Cewar Khalifa Sanusi Lamido.
An yi wa fursunoni 72 afuwa a gidajen yarin Zariya. Qatar ta ce tana ƙoƙarin sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.
Amurka tace jinkiri wajen amincewa da kudaden tallafin yakin Ukraine murkushe Kiev ne.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojojinta 80 tun bayan fara kai farmakin da suke kai wa Gaza.
Kotun Ghana ta tura ‘yar China gidan yari kan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp