Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu yace lokacin yajin aiki a makarantu a Najeriya ya zo karshe yayin da gwamnatinsa za ta fara aiwatar da shirin bai wa dalibai lamunin karatu a watan Janairun 2024.
Najeriya ta yi nasara a karar da ta daukaka kan wani hukunci dake neman ta biya diyyar dala biliyan 11 ga wani kamfanin kasashen waje bayan rushewar wata kwangilar shimfida bututun iskar gas.
Ɗaruruwan mahadda Al-Kur’ani mai girma sun yi cikar kwari a gidan Sanata Kwankwaso dake Miller Road a Kano domin tantancewa tare da daukar nauyin karatunsu na addini.
Ɗalibi ɗan shekara biyu ya mutu bayan faɗowa daga benen makaranta a jihar Abia.
‘Yan bindiga sun afka cikin garin Ɗanmusa, a jihar Katsina inda suka harbe mutum 9, ciki kuwa har da tsohon shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa, Dauda Mai Iyali.
Tubabbun ‘yan daban da suka koma ‘yan sandan sa-kai sunce zasu kama gurbatattu.
An kama mutum 76 masu yunkurin auren jinsi a Gombe.
Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wata daliba ’yar aji 3 a Kwalejin Ilimi da ke garin Biliri ta Jihar Gombe.
Gwamnatin Zamfara ta bajekolin hujjojin yadda Matawalle ya yi sama da fadi da naira biliyan 6.78 na ginin filin jirgin sama.
Gwamnatin Legas ta rufe Babbar Kasuwar Alaba, a matsayin wani mataki da take dauka kan kasuwanni masu sakaci da tsaftar muhalli a jihar.
Babbar Kotun Jihar Adamawa ta sake dage gurfanar da Kwamishinan Zabe na Kasa na Jihar (REC) da aka dakatar, Barista Hudu Ari Yunusa, zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba.
Tsohon shugaban ma su rinjaye a majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yi nasara kan abokin hamayyarsa a kotun daukaka Kara.
Tarayyar Turai ta fara bin matakai don sanya wa Nijar takunkumi.
An kashe ɗan Birtanyia a harin da Hamas ta kai wa Isra’ila.
Ayari na uku ɗauke da agaji ya shiga Gaza daga Masar.
Sojojin Sudan sun amince su yi zaman sulhu da RSF a Saudiyya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ