Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Litinin 13/11/2023 – 29/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman

Yan fashin daji sun kashe ‘yan sa kai 6 a karamar Bungudu a jihar Zamfara.

Ana zargin wata matashiya da kashe ’yarta mai watanni 11 ta hanyar ba ta guba a Karamar Hukumar Logo ta Jihar Binuwai.

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ɗora alhakin kasa magance matsalar tsaro a Arewa maso Yamma kan wasu mutanen da suka maida harkar garkuwa da mutane hanyar samun kuɗi.

Zaben Bayelsa: APC ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓe.

Douye Diri na PDP ya lashe zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.

An samu hatsaniya tsakanin wakilan jam’iyyun APC da Accord a jihar Bayelsa.

Magoya bayan PDP sun zanga-zanga a Abuja kan soke zaben ‘yan majalisar wakilai na Filato.

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga sun ceto mutane a Katsina da Kaduna.

Hukumar Hisbah na zama da ’yan Kannywood a yau.

Saudiyya ta soke bizar fasinjoji 264 daga Kano da Legas bayan sun dira Jeddah.

Turkiyya na shirin kafa asibitocin wucin-gadi a Masar don kula da Falasɗinawa.

An ƙara kashe sojojin Isra’ila biyu a Gaza cikin su har da ɗan fim ɗin Netflix.

An harba makamai masu linzami zuwa cikin Isra’ila daga Lebanon.

An naɗa tsohon firaminista David Cameron sakataren harkokin wajen Birtaniya.

An kiyasta cewa fannin tattalin arzikin Isra’ila ya yi asarar ayyuka kusan dubu 950 tin bayan ɓarkewar rikicin Gaza a watan jiya, a cewar alkaluman hukuma.

An kori sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya daga muƙaminta.

Ma’aikatan lafiya sama da 4,000 suka bar Ghana zuwa aiki a kasashen Turai.

An nada Fabregas kociyan Como ta Italiya na rikon kwarya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *