Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Laraba 25/10/2023 – 10/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aikewa majalisar dattawa wasiƙa kan naɗin sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa (ICPC).

Kotun ƙoli ta tsayar da ranar Alhamis domin yanke hukunci kan ƙarar Atiku Obi suka ɗaukaka, suna ƙalubalantar hukuncin kotun ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa.

Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin zaɓe a jihohi tara.

Majalisar Dattawa ta rantsar da Amos Yohanna a matsayin sanatan Adamawa ta Arewa.

Wasu fursunoni 2 da ake zargi da laifin fashi da makami sun tsere daga gidan gyaran hali a Katsina.

Hukumar Alhazai ta bai wa jihohi wa’adin biyan kuɗin Hajji zuwa Disamba.

Kwalejin koyon aikin Jinya ta jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi, ta karyata batun korar dalibarta, Rahama Sa’idu, saboda TikTok makarantar ta ce ta sallame tane saboda ta fadi jarrabawa sannan ta yi fashin zuwa makaranta na tsawon lokaci ba tare da kwakkwaran dalili ba.

Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 18 ne suka tsallake rijiya da baya-baya a wani hatsarin Mota da ya rutsa da su a sashin doguwar gadar da ke kan titin Legas zuwa Ibadan.

Tsagerun ‘yan bindiga sun tare ‘yan gudun hijira, sun harbe su har lahira a jihar Benuwai.

Isra’ila za ta daina bai wa jagororin Majalisar Ɗinkin Duniya biza.

Shugaban MDD ya ce an yi wa kalamansa ‘mummunar fassara.

Birtaniya ta tura jirgi ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza.

Syria ta ce Isra’ila ta kashe sojojinta takwas.

An yiwa Andy Robertson tiyata a allon kafada, sakamakon raunin da ya ji lokacin da yake yiwa Scotland wasa in ji Jurgen Klopp.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *