Daga Baba Usman Gama
Sojoji sun ceto daliban Jami’ar Gusau wadanda aka sace jiya da daddare.
Aƙalla sama da mutum 100 da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne suka mutu a wani hari da jiragen yaƙin sojoji suka kai a jihar Borno.
Jagoran mabiya ƙungiyar Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ya samu digirin digir-gir daga jami’ar Tehran ta ƙasar Iran.
Kingiyar SERAP ta buƙaci majalisa ta yi watsi da ƙudurin lura da shafukan sada zumunta a Najeriya
Dubban mutane a Maroko sun gudanar da zanga zangar lumana a gaban majalisar kasar, domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.
Kungiyar Hamas ta sanar da kai sabon hari birnin Ashkelon na Isra’ila domin mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Falasdinawa.
Kamfanin Ferrari zai soma karbar kirifto domin sayar da motoci.
Amurka ta ce daga gobe Litinin jirgin ruwanta zai fara kwashe ‘yan kasarta daga Isra’ila.
Fafaroma Francis ya nemi a buɗe ƙofofin kai agaji a Gaza.
‘Yan Isra’ila da suka mutu sun kai 1,400.
Jagoran siyasar Hamas ya gana da ministan wajen Iran.
Afghanistan ta fuskancin girgizar ƙasa karo na uku cikin mako guda.
Mali ta aike da dakarunta gami da sojojin hayar Wagner zuwa arewacin kasar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo