Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Juma’a 15/12/2023 – 01/06/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Sojoji sun samu nasarar lalata mafakar yan bindiga da dama tare kashe yan bindiga 5 tare da kwato makamai jihar Zamfara da Sakkwato.

Kotun ƙolin Najeriya ta ce dole Nnamdi Kanu ya fuskanci shari’a.

Sojoji sun kashe ƴan bindiga tare da kuɓutar da mutum shida a Sokoto.

Babbar jojin jihar Niger ya yake hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi da ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar cinna mata wuta.

Wasu kwamishinonin Rivers shida sun sake ajiye aiki yayin da rikicin siyasa ke daɗa ƙamari a jihar.

AA Zaura ya dora alhakin faduwa zaben 2023 da APC ta yi a Kano kan gwamnatin Buhari.

Awanni bayan ya bar Buhari a garin Daura, tsohon Gwamnan jihar Kaduna El Rufa’i ya sa labule da Janar IBB a Minna.

Mutane 16 sun rasu, wasu 30 sun samu rauna a hatsarin babbar mota a yankin Riyom da ke Jihar Filato.

Gwamnan Jihar Anambra na farko Chukwuemeka Ezeife ya riga mu gidan gaskiya.

Manyan ‘yan Majalisar Tarayya guda biyu sun yi tattakin nuna goyon baya ga Gwamna Fubara na jihar Rivers a yau Juma’a.

Kamfanin simintin Dangote ya ba da tallafin karatu ga dalibai 119 a jihar Ogun.

Wani magidanci ya rataye kansa a yankin Jimeta da ke Jihar Adamawa.

An gurfanar da wani daraktan kamfanin Faris, Salisu Suleiman a gaban kotu kan zargin karkatar naira miliyan 21 a jihar Kano.

Nijar da Mali da Burkina sun kulla yarjejeniyar yaki da ta’addanci.

Tsohon shugaban Zambiya ya garzaya kotu don ƙalubalantar janye masa hakkoki.

Kotun Ecowas ta umarci sojoji su saki Bazoum nan take.

An gano gawawwakin sojin Isra’ila biyu a Gaza.

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Ghana.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *