Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Juma’a 10/11/2023 – 26/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya yi alhini kan mutuwar mace Manjo Janar ta farko a Najeriya.

Sojojin Najeriya sun hallaka ‘yan ta’adda 113 a cikin mako guda.

INEC tace ‘za a wallafa sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓen gwamna a Bayelsa, Kogi da Imo’

Hedkwatar Tsaro tace sojoji sun kashe ’yan bindiga 113, sun kama mutum 300 a cikin mako 1.

Nuhu Ribadu ya tabbatar da samar da cikakken tsaro a zabukan gwamna na Kogi, Bayelsa da Imo.

An jibge jami’an tsaro 40,000 albarkacin zaben gwamna a Kogi.

Kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da nasarar Gwamnan jihar Enugu Peter Mbah na jam’iyyar PDP.

Shugaban Karamar Hukumar Lokoja ya rasu ana jajiberin Zaben jihar Kogi.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta nemi Jarumai da Masu Shiryawa da Ba da Umarnin Fina-finan Hausa su kai kansu gabanta ranar Litinin 13-11-2023 da karfe 2 na rana.

Rundunar ‘yan sanda ta tarwatsa wasu mata da ke zanga-zangar dole a cire kwamishinan ‘yan sanda a jihar Bayelsa.

Mazauna Lokoja sun koka kan tsadar rayuwa gabanin zaɓen gwamna.

Mutum biyu sun jikkata yayin da Hamas ta harba rokoki birnin Tel Aviv.

Saudi Arabia ta soki irin ruwan wutar da Isra’ila ke yi a yankin Gaza.

An kashe mutane 700 cikin kwana biyu a Sudan.

Gaza: Iran ta yi barazanar shiga yakin Isra’ila da Hamas.

Cutar mashaƙo ta ɓarke a wani gidan yarin Afirka ta Kudu.

Ambaliya ta lalata wata babbar gada a kudu maso yammacin Somaliya.

Likitoci a New York sun yi aikin dashen ido karon farko a duniya.

Sir Jim Ratcliffe na daf da sayen hannun jari a Man United.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *