Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Juma’a 08/12/2023 – 24/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Hukumar Shari’a ta Kasa (NJC) ta dakatar da Mai Shari’a S.O Falola na Babbar Kotun Jihar Osun tare da neman a yi masa ritayar dole kan laifin saba ka’idar aiki da kuma bayar da umarnin kotu ta hanyar da ba ta dace ba.

Sojojin Najeriya sun kama jirgin ruwa ɗauke da gangar mai fiye da 3,000 na sata.

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i da Khalifan Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II, sun kai ziyara garin Tudun Biri a jihar Kaduna.

Matatar Dangote ta tabbatar da cewa ta fara karɓar ɗanyen man fetur wanda za ta fara tacewa domin samar da man fetur da sauran abubuwan amfani.

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta umarci lauyoyinta su bibiyi wata takarda da suka ce tana yawo a shafukanta sanda zumunta da ke cewa kotu ta bayar da umarnin rufe asusun gwamnati.

Sheikh Bala Lau yayi da a biya mutanen Tudun Biri diyya, kuma a buɗe iyakar Najeriya da Nijar.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya ce zasu matsa har sai an yi wa mutanen kauyen Tudun Biri adalci.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutane 2 da ake zargi da yin garkuwa da wani mai suna Musa Abdullahi a Gombe.

Lauyan ’yan kasuwar Kano masu shaguna a Filin Idi na Kofar Mata, Nuruddeen Ayagi, ya ce umarnin biyan diyyar Naira biliyan 30 da kotu ta ba wa gwamnatin jihar yana nufin rufe asusun gwamantin da ke bankuna.

Yayin da ake tunkarar hukuncin kotun koli kan zaben gwamnan jihar Kano, manyan jam’iyyu biyu sun ƙara jaddada matsayar tabbatar da zaman lafiya.

Ƙasar Afrika ta Kudu ta kama mutane 133 da ake zargi da safarar mutane.

Putin zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa karo na biyar.

Ana kasa da makwanni buyu, matsaloli sun dabaibaye shirin zaben kasar Jamhuriyar Demkradiyar Congo.

Dan wasan Man. United Maguire ya lashe kambin dan wasan Gasar Premier na watan Nuwamba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *