Daga Baba Usman Gama
Sojojin sun ce sun kama ’yan Boko Haram 2 a Gezawa tare da tarin makamai, a kokarinsu na yunkurin kaddamar da wani mummunan hari a Kano.
Kungiyar ƙwadago za ta shiga yajin aiki sanadiyyar ‘kama shugabanta’.
Giwaye daga kasar Kamaru na ci gaba da zama barazana ga manoma a Borno, lamarin da ya sa majalisar dokokin tarayya ta mika kuka ga shugaba Tinubu.
Dala ta na karyewa a kasuwar canji bayan CBN ya fara sallamar bankuna bashin kudin waje da su ke bi.
JTF ta kama jirgin ruwa maƙare da litar gas 300,000 na sata.
Gwamnatin jihar Kano ta kara wa ma’aikata 231 girma a wasu ma’aikatu da hukumomin jihar.
Rundunar sojin sama ta halaka ƴan ta’adda sama da 160 a wani samame ranar 2 a jihohin Borno da Yobe.
Wani matashin magidanci ɗan shekara 25 a duniya, Ibrahim Ahmadu, ya rasa rayuwarsa yayin ƙokarin ceton matarsa, Amina Sani, daga sharrin ƴan daba.
Sakamakon hatsarin wata trela da adai-daita sahu, mutane 8 sun mutu yayin da 10 suka jikkata a Mpape, Abuja.
Kotu ta umarci EFCC ta saki Emefiele ko ta gurfanar da shi.
Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta tabbatar da nasarar Sanata Jibrin Isah a daga Kogi ta gabas.
Babbar kotun Tarayya a jihar Kano ta dakatar Gwamna Abba Kabir na jihar Kano na daukar mataki kan makarantu ma su zaman kansu.
Mahukuntan Najeriya sun dakile fasakaurin ayaba zuwa Nijar.
Tunisia na shirin kafa dokar dauri kan duk wanda ya kulla alaka da Isra’ila.
Nijar ta kaddamar da bututun man da ta shimfida zuwa Benin.
Zakir Naik ya ba Falasdinawa tallafin Naira militan 383.
Rwanda ta ɓullo da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga duk ‘yan Afirka.
Mummunar ambaliyar ruwa a Kenya ta shafe wasu tituna a wasu garuruwan ƙasar, tare da yin awon gaba da ababen hawa.
Rasha ta kai hare-hare ta sama a arewa maso gabashin Ukraine.
Shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah ya gargadi kasar Amurka cewar muddin Isra’ila taki daina kai munanan hare hare a Gaza, fadan zai rikide zuwa yakin Gabas ta Tsakiya baki daya.
Diaz ya koma atsisaye yayin da mahaifinsa ke hannun masu garkuwa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp